<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>11</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Maɗaukakin Sarki madauwami ne,
 Kai ne kuma mafarin hikima duk.
 Walƙiyar darajarka ta makanta mu,
 Mai iko, mai nasara, ya Allahnmu.

[V2]
 2) Mulkinka mai haske ya tabbata nan,
 A hankali, a natse saukowarsa.
 Albarkarka tana zubowa kanmu,
 Alheri mai yawa da nagartarka.

[V3]
 3) Kai ne mai rayad da talikanka duka,
 Da lafiya da ƙarfi da iyawa kuwa.
 Mun ga jamalinka cikin halitta,
 Gwanintar aikinka ka bayyana kuwa.

[V4]
 4) Da rana da wata har taurari kuwa,
 Kyawawan tafukka, da Kogin Kwara,
 Da duwatsu duk da tuddai suna yi
 Wa  sunanka yabo, ya Mahalicci.

[V5]
 5) Ya Ubangiji mai girma, Mai Tsarki ne kai; .
 Allah ne na zurfafa da al'arshi,
 Mala'ikunka suna yin sujada,
 Mu fa sai biyayya za mu yi maka.</lyrics>
<title>Maɗaukakin Sarki Madauwami Ne LW11</title>
<author>Welsh, Roberts, John (1822-1877), Smith, Walter Chalmers (1824-1908)</author>
</song>